Marigayi Muhammad Ali ya yi fama da cutar makyarkyatan jiki mai suna Pakinson na tsawon shekaru 32 wadda ake danganta ta da irin duka da aka rika yiwa fuskar sa.
Ya rike kambun wannan dambe na duniya na tsawon shekaru samada 30, ana karawa dashi yana samun nasara.
A wannan mako aka kwantar dashi a wani asibiti dake Phoenix, Arisona saboda laulayi a makogoron sa.
Sunan san a ainihi shine Cassius Clay kafin shekara ta 1964 ya koma Muhammadu Ali bayan ya musulunta.288